Mikel Obi ya godewa 'yan Najeriya

Image caption Dan wasan Najeriya John Mikel Obi

Dan wasan Najeriya John Mikel Obi ya bayyana farin cikinsa dangane da halayyar da 'yan Najeriya suka nuna masa a lokacin da aka sace mahaifinsa.

A watan daya gabata ne dai wasu mutune suka sace Michael Obi suka kuma yi garkuwa da shi har na kusan makwanni biyu, lamarin daya janyo cece kuce a kasar.

Sai dai daga bisani an kame mutanen da suka sace shi a jihar Kano.

A cewar Mikel, wannan al'amari yasa ya dauki darasi matuka na irin kaunar da 'yan Najeriya ke masa.

Ya kara da cewa zai ci gaba da sadaukar da rayuwarsa wajen taka muhimmiyar rawa a duk lokacin da zai bugawa kasarsa wasa, wanda hakan yasa ya yi gaggawar amsa gayyatar da aka yi masa na zuwa don buga wasan da kungiyar ta Super Eagles za su kara da Madagascar.