Tennis: Djokovic ya doke Carlos Berlocq

Novak Djokovic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak Djokovic lokacin da ya lashe gasar Australian Open

Dan wasan Tennis na daya a duniya Novak Djokovic ya lallasa Carlos Berlocq na Argentina da ci 6-0 6-0 6-2, a gasar cin kofin US Open.

Djokovic ya sha kashi a wasanni biyu kacal a bana - a wani abu da akewa kallon daya daga cikin shekaru mafiya kayatarwa a fagen kwallon Tennis.

Berlocq, wanda ke mataki na 74, bai iya kama kafar dan kasar ta Serbia ba.

Roger Federer wanda ya taba lashe gasar har sau biyar ya doke Dudi Sela da ci 6-3 6-2 6-2.

Sai dai hakan ba wani abin kayatarwa ba ne idan aka kwatanta da rawar da Djokovic ya taka a filin wasan na Arthur Ashe daga bisani.