Rugby: Kyaftin din Ingila Moody ya samu rauni

Lewis Moody Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moody na daga cikin kwararrun 'yan wasan Ingila

Kyaftin din tawagar kwallon zari-zuga ta Rugby na Ingila Lewis Moody ba zai taka leda a wasan farko da za su kara da Argentina ba a gasar cin kofin duniya ta Rugby.

Dan wasan dai yana fama ne da rauni a gwiwarsa, don haka shi da wasan na ranar Asabar sai dai kallo.

Lewis Moody mai shekaru 33 ya samu raunin ne a wasan sada zumuntar da Ingila ta fafata da Wales a Twickenham ranar 6 ga watan Agusta.

Moody ya taba samun rauni a gwiwar ta sa lokacin da yake takawa kulob dinsa na Bath leda a watan Janairu abinda ya sa bai buga gasar Six Nations ba.

A ranar Alhamis ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar taka leda domin tabbatar da lafiyarsa a wasan da za su fafata da Pumas.