Nadal ya fadi a gaban manema labarai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rafeal Nadal ya fadi ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai

Mai kare kambun gasar US Open, Rafael Nadal ya fadi a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan da ya doke David Nalbandian a zagaye na uku.

Dan wasan Tennis din mai shekarun haihuwa 25 ya buga wasan ne cikin matsananci zafin rana a filin wasan na Arthur Ashe.

Dan wasan dai ya fadi ne sanadiyar daurewar jijiya bayan gajiyar da ya yi a wasan.

Bayan dai an duba lafiyarsa na tsawon mintuna 15, dan wasan Tennis din ya ci gaba da ganawar da yake yi da manema labarai.