Rajevac na neman aikin kocin Masar

Image caption Milovan Rajevac

Tsohon kocin Ghana Miolvan Rajevac na cikin wadanda ke takarar neman aikin kocin tawagar kwallon kafan Masar.

Kocin ya isa birnin alhkahira ne a ranar Litinin domin ya tattauna da Hukumar kwallon Masar.

An dai sanya sunansa cikin jerin sunayen masu neman aikin, tare da tsohon kocin Amurka Bob Bradley.

Rajevac ya taimakawa tawagar Ghana inda ta kai matakin wasan dab da kusa dana karshen a gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Afrika ta kudu da kuma wasan karshen a gasar cin kofin Afrika duk a shekarar 2010.

Kocin dai yaki ya kara wa'adin kwantaraginsa da Ghana, inda ya koma wata kungiya a kasar Saudiyya, kafin ya koma jogarantar kasar Qatar, inda kuma aka sallame shi a watan daya gabata.