UEFA: Wenger bai yi nasara ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger bai yi nasarar kalubalantar dakatarwar da Uefa ta yi masa ba a gasar zakarun Turai.

Hukumar Uefa dai ta samu Wenger da laifi ne bayan da ya tattauna da jami'an Arsenal din da ke kan benci, bayan ta haramta masa yin hakan a wasan da Arsenal ta doke Udinese da ci daya da nema.

Har wa yau anci tarar Arsenal euro dubu goma, saboda rashin da'a.

A yanzu haka dai Wenger bai zai halarci wasanni da Arsenal za ta buga da Borussia Dortmund da kuma Olympiakos ba a gasar zakarun Turai.