US Open: Federer ya doke Juan Monaco

roger federer
Image caption Federer ya lashe gasar US Open sau biyar a baya

Roger Federer ya lallasa Juan Monaco da ci 6-1 6-2 6-0 a ci gaba da gasar cin kofin US Open inda ya tsallake zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe.

An samu jinkiri kafin fara wasan na su domin kammala wasan matan da aka fafata.

Federer ya taka rawar gani sosai, inda ya lashe wasan da ci 6-1 6-2 6-0 cikin mintina 82.

Tun da farko jagoran Tennis na duniya Novak Djokovic ya doke dan Ukraine Alexandr Dolgopolov inda shi ma ya tsallake zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe.

Mai yiwuwa Djokovic ya fafata da Roger Federer a wasan kusa da na karshe, idan kowannensu ya yi nasara a wasansa na gaba.