Argentina ta doke Najeriya da ci uku da guda

Image caption A wasan da kasashen biyu su ka buga a Abuja, Najeriya ce ta yi nasara da ci 4 da 1

Dan wasan Real Madrid Gonzalo Higuain ya zura kwallaye biyu a wasan sada zumuncin da Argentina ta doke Najeriya da ci uku da daya.

Kyaftin din tawagar Argentina a wasan, ya samarwa Higuain passing din da ya zura kwallon farko ana minti 24 da wasan.

Sai kuma Angel Di Maria da ya zura ta biyu bayan minti biyu da aka zura ta farko.

Ana dawowa Hutun rabin lokaci ne dai Chinedu Obasi ya fanshe kwallo guda, amma ana sai kuma Higuain ya kara zura wata kwallo ana minti 65.