'Ingila ta yi sa'a'- Capello

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabio Capello

Kocin tawagar kwallon kafan Ingila, Fabio Capello ya amince cewa sa'a ce kawai Ingila ta samu a nasarar da ta yi akan Wales.

Ingila dai ta doke Wales ne da ci daya da nema.

Capello ya ce 'yan wasansa basa buga wasa da kwarin gwiwa a filin wasa na Wembley.

Ashley Young ne dai ya zura kwallon da ta ba Ingila nasara ana minti 35 da wasan, nasarar da ta zamawa Ingila ta farko a filin na Wembley wajen sama da shekara guda kenan.

Ingila dai a yanzu haka tana neman maki guda ne tal domin tsallake zuwa gasar cin kofin Turai da za'a yi a Poland da Ukraine a badi.

Tawagar Ingila dai za tayi tattaki ne zuwa Montenegro.

Ingila dai ba ta taka rawar gani ba a wasan da ta buga da Wales a filin Wembley duk da nasarar da ta samu.