Uefa za ta tsaurara hukunci game da kashe kudi

Hukumar kwallon kafan Turai, Uefa ta ce ba za rika bada kyautan kudi ba, ko kuma za ta haramtawa kungiyoyin siyan 'yan wasa inda basu bi ka'idojin kashe kudi ba.

Hukumar ta ce idan kuma kungiya ba ta yi nadama ba, za ta dakatar da ita daga dukkan harkar kwallon kafa a Turai.

"Yana da mahimmaci cewa Uefa tana tunanin hukuncin da za'a yiwa kungiyoyi idan sun keta ka'idojinta." Inji wani babban jami'in, Inter Milan Ernesto Paolillo.

"Ya ce sabuwar dokar ta Uefa za ta taimakawa kananan kungiyoyin wadanda basu da karfin siyan 'yan wasa masu tsada."

"Bai kamata ace koda yaushe kungiya tana siyan 'yan wasa ba." In ji Karl-Heinz Rummenigge shugaban Bayern Munich.

Kungiyoyi da dama dai a Turai, suna kashe makudan kudade wajen siyan 'yan wasa, alhalin suna fama da basusuka.

Kashi 20 ne kawai ciki dari na kungiyoyin Turai ke samu riba.