Ayew zai yi jinya na tsawon kwanaki 10

Image caption Andre Dede Ayew

Dan wasan Ghana Andre 'Dede' Ayew zai yi jinya na tsawon kwanaki goma bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta buga da Brazil a ranar Litinin din da ta gabata.

Raunin da dan wasan ya samu ya zama babban koma baya ga kungiyarsa ta Marseille dake Faransa.

Ayew ya taka rawar gani sosai a gasar Faransa a bara.

A yanzu haka dai ba zai taka leda ba a wasan da kungiyarsa za ta kara da Rennes a ranar asabar da kuma a gasar zakarun Turai da Olympiakos a Athens.

Tun da aka dawo kakar wasan bana a Faransa, Marseille ba ta lashe wasa ko guda ba, inda take matsayi na goma sha shida.