Klistschko ya ce zai yiwa Adamek kisan gwani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vitali Klitschko

Zakaran wasan damben zamani wato Boxing na WBC Vitali Klitschko ya ce zai inganta tarihinsa a harkar dembe a karawarsa da Tomasz Adamek.

Klitschko zai fafata ne Adamek a Poland a ranar asabar, inda ya sanya kambunsa na WBC.

Klitschko dai yayi kisan gwani sau 39 a dembe 42 da ya lashe.

"Zan yi iyakacin kokari na inga na inganta tarihi na na kisan gwani a demben." In ji Klitschko.

"Na dai yi alkawarin zan yi galaba akan Adamek a wasan."