Dan Zidane ya yi horo da babbar tawagar Madrid

Dan Zinadine Zidane Enzo Hakkin mallakar hoto goggle
Image caption Ana saran Enzo ya takawa Real Madrid leda nan gaba kadan

Shafin intanet na Real Madrid ya ce dan Zinadine Zidane Enzo, ya yi horo tare da manyan 'yan wasan Real Madrid irinsu Ronaldo da Ozil da kuma Kaka. Mahaifinsa wanda daraktan wasanni ne a Real Madrid, ya kalli horon ne tare da koci Jose Mourinho a filin horo na Valdebebas.

Enzo, wanda ke taka leda a tsakiya, ya haskaka a horon inda ya rinka karbar umarni daga Jose Mourinho.

Zidane dai ya taka leda a Real Madrid tsakanin shekarun 2001 da 2006, kuma ya taka rawar gani bayan da ya zo Bernabeu daga Juventus.

Enzo, mai shekaru 16 yana takawa babbar tawagar matasa ta Madrid ne kwallo - kuma yana da kwarewa sosai kamar ta mahaifinsa. Akwai kannensa biyu da ke taka leda a Madrid din.

Sai dai ana ganin zai yi wuya ya takawa Faransa leda, ganin yadda tuni Spain ta fara zawarcinsa.