'Zidane ya taimakawa Benzema' - Mourinho

Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya alakanta irin taka rawar da Benzema ya nuna a nasarar da kungiyar ta yi akan Getafe ga Zinedine Zidane.

Mourinho ya ce Zidane ya taimaka matuka musamman wajen kwarin gwiwar da yake ba Benzema bayan kwallaye biyun da ya zura a nasar da kungiyar ta yi da ci hudu da biyu a wasan.

Cristiano Ronaldo da kuma Gonzalo Higuain duk sun zura kwallo a wasan.

Mourinho dai ya yaba da irin bajintar da dan wasan ya nuna a wasan.

"Ya kamata a yabawa Benzema, saboda irin taka rawar ganin da yake yi a yanzu kuma ina ganin abokan wasansa ne da kuma Zizou ke taimaka mishi." In ji Mourinho