Wenger ya nuna farin ciki ga sabbin 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya yaba da irin gudunmuwar da sabbin 'yan wasansa suka bada a nasarar da kungiyar ta yi akan Swansea a gasar Premier.

Arsenal dai ta doke Swansea ne da ci daya mai ban haushi, kuma Andre Asharvin ne ya zura kwallon.

Wenger dai ya fara ne da dan wasan bayan da ya siyo daga Jamus, Per Mertesacker da kuma Mikel Arteta da ya siyo daga Everton.

Wenger ya ce: "Mertesacker ya nuna natsuwa, kuma ya taimakawa 'yan wasan baya matuka."

"Arteta kuma ya taka rawar gani, musamman ma kafin a tafi hutun rabin lokaci. Ya dai dan fuskanci matsala bayan da aka dawo, amma ya yi matukar kokari."