'Ina so in zama Maradonan City'- Aguero

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sergio Aguero

Sergio Aguero ya ce yana son ya rika taka leda a City kamar yadda Diego Maradona ya taka leda a Napoli.

Irin rawar da Aguero ke takawa a City na nuni da cewa kwaliya ta fara biyan kudin sabulu a yayinda ya riga ya zura kwallaye shida a wasanni hudu da ya bugawa City.

Dan wasan ya shaidawa jaridar The Mirrow cewa: "Ina fatan zan taimakawa Manchester City ta haskaka kamar yadda Diego ya yi a Napoli.

"Na zo kungiyar ne domin in taimaka mata wajen lashe kyautuka. Idan mui lashe kyautuka a gasar bana zai yi kyau."

City dai ta fara gasar Premier ta bana da kafar dama, inda ta lashe wasanni hudu da ta buga a gasar gabaki daya.