Davies ya baiwa Cleverly hakuri

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tom Cleverly bayan ya samu rauni

Kyaftin din Bolton Kevin Davies ya baiwa dan wasan Manchester United Tom Cleverly hakuri, saboda raunin da ya samu bayan ya tade shi a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a gasar Premier ta Ingila a karshen mako.

Matar Davies, Emma, ta rubuta a shafinta ba twitter cewa: "Ga duk wadanda ke adawa da mijina.. Kevin ya yi magana da Tom Cleverly ta wayar tarho, kuma ya bashi. Ba zai taba raunata wani da ganganba."

Cleverly ya samu raunin ne ana minti biyar da fara wasan da United ta yi nasara akan Bolton da ci biyar da nema.

A yanzu haka dai dan wasan zai yi jinya ne na wata guda.