UEFA: Ramsey ba zai taka leda a wasan Dortmund ba

Image caption Aaron Ramsey na takawa Arsenal leda

Dan wasan Arsenal Aaron Ramsey ba zai samu taka leda ba a wasan da kungiyarsa za ta buga da Borussia Dortmund a gasar zakarun Turai, a ranar Talata.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa dan wasan mai shekarun haihuwa 20 ya samu rauni ne a lokacin da kungiyar ke horo.

Dan wasan dai bai samu zuwa Jamus ba da sauran tawagar kungiyar.

Arsenal dai na fuskantar matsalar 'yan wasan tsakiya saboda shima Jack Wilshere yana jinyar raunin da ya samu a gwiwarsa.