Sam Stosur ta lashe gasar US Open

Sam Stosur
Image caption Rabon da 'yar Australia ta lashe US Open tun 1972

'Yar kasar Australia Sam Stosur ta lashe gasar US Open bayan da ta doke Serena Williams ta Amurka.

Sam Stosur, wacce ita ce ta tara a jerin 'yan wasan da suka shiga gasar, ta taka rawar gani da ci 6-2 6-3.

Sai dai Williams na fuskantar hukunci bayan da ta gayawa alkalin wasan Eva Asderaki cewa: "kin wuce gona da iri" kuma kina nuna kiyayya."

Williams wacce ta lashe babbar gasar Tennis ta Grand Slam sau 13, ta harzuka ne bayan da Asderaki da bayar da maki ga abokiyar karawarta.

Stosur, 'yar shekaru 27, daga jihar Queensland ta zamo mace ta farko daga Australia da ta lashe gasar US Open tun bayan Margaret Court a shekarar 1973.

Ta lallasa Williams ne cikin sa'a guda da minti 13 a Flushing Meadows.