Maputo: 'Yan tseren Najeriya sun taka rawar gani

Hakkin mallakar hoto aaf
Image caption 'yar tseren Najeriya, Damola Osayomi

'Yan tseren Najeriya mata sun lashe zinari da azurfa da kuma tagulla a tseren mita dari a gasar wasanni ta Afrika da ake yi a birnin Maputo na kasar Mozambique.

Damola Osayomi ce ta zama ta farko sannan Blessing Okagbare ta zama ta biyu a yayinda Gloria Asunmu ta zama ta uku.

A baya dai an dakatar da Osayomi na tsawon watanni shida bayan an same ta laifin shan haramtattun kwayoyi. '

Yar tseren da kuma shaidawa BBC yadda ta ji alokacin da aka dakatar da ita;

"Gaskiya ban ji dadi ba a wannan lokacin, na dauka a wannan lokacin na daina tsere kenan, ina matukar farin ciki da dawo tsere, kuma da yardar ubangiji nayi nasara daga dawowa na." In ji

A tseren mita dari na maza dan kasar Masar Amr Seoud ne ya lashe zinari sai kuma Youssef Meite dan kasar Ivory Coast ya lashe azurfa a yayinda dan Najeriya Obinna Metu ya lashe tagulla.