'Real Madrid da Barcelona sunfi sauran kungiyoyi'- Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce irin kudin da kungiyar Real Madrid da Barcelona ke da su sun sanya kungiyoyin biyu gaban kowacce kungiya a nahiyar Turai.

Kocin Arsenal din ya bayyana Chelsea da kuma Manchester City a cikin manyan kungiyoyi a Turai da za su iya siyan kowani irin dan wasa komi tsadansa.

"Nayi imanin cewa a kakar wasan bana akwai kungiyoyin biyu wato Real Madrid da kuma Barcelona dake gaban kowacce kungiya. Duk sauran kungiyoyin sai su biyo bayan su." In ji Wenger

"Mu dai yanzu muka fara kuma muna da sabbin 'yan wasa, mu dai muna kokari ne mu wuce zagaye na farko a gasar zakarun Turai."