'Arsenal ta dawo kan ganiyar ta' - Rice

Image caption Dan wasan Arsenal Van Persie

Mataimakin kocin Arsenal Pat Rice ya ce kungiyar ta dawo kan ganiyar ta bayan da ta buga daya da daya da Borussia Dortmund a gasar zakarun Turai.

Kungiyar dai ta kusan ta kammala wasan da maki uku, kafin Ivan Perisic ya fanshewa Dortmund ana sauran minti biyu a tashi wasan.

Rice ya ce; "Nasarar da muka samu akan Swansea a karshen mako ne ya kara mana kwarin gwiwa, gashi kuma an sayo kwararrun 'yan wasa.

"Mun taka rawar gani sosai a wasan da muka buga a Jamus, abun da kuma yasa nayi imanin cewa mun fara haskakawa kenan."

Arsenal dai ta fara fuskantar matsala ne a kakar wasan bana, bayan ta sha kashi a hannun Liverpool da Manchester United.