Zakarun Turai: Barca ta buga 2-2 da AC Milan

Zakarun Turai: Barca ta buga 2-2 da AC Milan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pedro Rodriguez ne ya ramawa Barcelona a minti na 36

Kwallon da dan wasan AC Milan Thiago Silva ya zira a mintin karshe ta baiwa Milan damar rike mai rike da kanbun Barcelona a filin wasa na Nou Camp inda aka tashi 2-2.

Pato ne ya fara zira kwallo bayan dakika 24 da fara wasan, kafin Pedro Rodriguez ya ramawa Barcelona a minti na 36.

Ana minti na 50 ne kuma David Villa ya zira kwallo ta biyu abinda ya baiwa Barcelona damar jagoranci da 2-1.

Sai dai Milan ta farke bayan da Silva ya zira kwallo da ka daga kwanar da Clarence Seedorf ya buga.

Kwallon tasa ita ce ta 9 da 'yan wasan Brazil suka zira a daren Talata a gasar ta zakarun Turai.

A sauran wasannin kuwa, FC Porto ta lashe Shakhtar Donetsk da ci 2-1 yayin da Marseille ta yi nasara kan Olympiakos da ci 1-0.

Viktoria Plzen sun tashi 1-1 a gida da BATE Borisov. Sai Chelsea da ta doke Bayer Leverkusen da ci 2-0.

Ga sakamakon wasannin gaba daya

Genk 0 - 0 Valencia Chelsea 2 - 0 Bayer Leverkusen Olympiakos Piraeus 0 - 1 Olympique Marseille Borussia Dortmund 1 - 1 Arsenal Porto 2 - 1 Shakhtar Donetsk APOEL 2 - 1 Zenit Barcelona 2 - 2 Milan