'Mun shiryawa Manchester United'- Villa Boas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya ce kungiyarsa za ta fuskanci kalubale na dabam a wasan da kungiyar za ta kara da United a ranar lahadi.

David Luiz da Juan Mata ne su ka zura kwallayen biyu da Chelsea ta yi nasara akan Bayer Leverkusen a gasar zakarun Turai, a ranar Talata.

Saboda tattakin da Chelsea za ta kai United, Villas-Boas ya hutar da kyaftin din kungiyar John Terry da kuma Frank Lampard, amma Frank Lampard din ya shigo daga baya.

Villas-Boas ya ce: "Za mu kokari mu yi nasara a ziyarar da zamu kai United. Wasan zai kayatar."

Ya kara da cewa: "Zamu hadu ne da United a lokacin da suke kan ganniyar su.

"Sun taka rawar ganin sosai a farko kakar wasan bana, inda ma suka fi kokari bisa yadda su ka murza leda a bara, ina ganin wannan babban kalubane ne gare mu, kuma mun shirya musu tsaf".

A team that has made its impact at the beginning of the Premier League is different from last year, but I think it provokes in us a good challenge.

"Muna da kwarin gwiwa za mu je Old Trafford mu yi nasara."