Iniesta zai yi jinya na tsawon wata guda

Image caption Andres Iniesta

Dan wasan Barcelona, Andres Iniesta ba zai taka leda ba na tsawon makwanni hudu saboda raunin da ya samu a wasan da kungiyarshi ta buga da AC Milan a gasar zakarun Turai.

Dan wasan ya fita ne a fili ana sauran minti biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda kuma Cesc Fabregas ya maye gurbinsa.

Barcelona dai ta buga biyu da biyu da AC Milan a filin Camp Nou.

Iniesta ba zai taka wasanni biyar nan gaba ba da Barcelona za ta buga, wanda kuma ya hada da karawar da kungiyar za ta yi da Valencia da Atletico Madrid da kuma BATE a gasar zakarun Turai.

Iniesta shine dan wasa na biyu da samu rauni a Barcelona, yayinda shima Alexis Sanchez zai yi jinya na tsawon makwanni takwas saboda raunin da ya samu a wasan da kungiyar ta buga da Real Sociedad a karshen mako, inda su ka tashi biyu da biyu.