Fifa ta yi watsi da daukaka karar da Bin Hammam ya yi

Image caption Muhammed Bin Hammam

Hukumar kwallon kafa ta duniya-Fifa ta yi watsi da daukaka karar da Mohamed bin Hammam ya shigar a gabanta bayan dakatarwar da ta yi mishi daga dukkan harkar kwallon kafa har abada.

Hukumar dai ta dakatar da shine saboda zargin da ake mishi na kokarin bada cin hanci, domin a kada masa kuri'a a zaben shugaban hukumar da ya tsaya takara.

Fifa ta ce wani kwamitin mai membobi uku da ta kafa ya gana na tsawon sa'o'i bakwai kuma ya amince da sallamar da kwamitin da'a ya yiwa Bin Hammam daga harkar kwallon kafa.

A baya dai Bin Hammam ya ce zai kalubalanci hukunci a kotun daukaka karar wasanni.

Amma dai sai ya fara daukaka kara a Fifa, idan bata amince bane sai ya kai kokensa kotun daukaka karar wasanni ta duniya.

Bin Hammam, dai ya musanta zargin da ake yi masa na kokarin ba membobin hukumar Caribbean cin hanci domin su kada mashi kuri'a.

Daga baya dai Bin Hammam bai tsaya takara ba Blatter, wanda ya tsaya shi kadai kuma ya lashe zaben.