'Ba za mu tursasawa Gerrard dawowa ba' - Dalglish

Image caption Steven Gerrard

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya ce kungiyar na taka tsan-tsan kafin su bar Steven Gerrard ya dawo taka leda, saboda jinyar da ya yi.

Dan wasan mai shekarun 31 na shirin dawowa taka leda ne a wasan da kungiyar za ta buga da Tottenham a karshen mako bayan ya yi jinyar rauni na tsawon watanni shida.

Amma akwai yiwuwar kyaftin din kungiyar ba zai samu buga wasan ba da kuma wasan cin kofin Carling da kungiyar za ta buga da Brighton a ranar Laraba.

"Ba wani hanzarin da muke a bangaren mu, kuma shima ba hanzari yake ba, dolene muyi taka tsan-tsan." In ji Dalglish.

Ya kara da cewa: "Duk wanda muka bukace shi da ya buga wasa, sai mun tabbatar da cewa yana da koshin lafiya."

"Zamu duba lafiyarsa sosai kafin mu tantance ko zai iya dawowa taka leda."

Gerrard bai taka leda ba tun a watan Maris din da ya gabata bayan tiyatar da aka yi mishi sanadiyar raunin da ya samu.