Ina son na zamo shugaban Barca - Gerard Pique

Gerard Pique
Image caption Gerard Pique yana taka leda sosai a Barcelona

Dan wasan Barcelona Gerard Pique ya ce yana fatan wata rana ya zamo shugaban kulob din idan ya gama taka leda a rayuwarsa ta kwallo.

Sandro Rosell shi ne shugaban Barcelona na yanzu bayan da ya maye gurbin Joan Laporta a kakar wasa ta 2010.

Kuma Pique na fatan wata rana zai gadi Rosell a matsayin jagora a kulob din na Camp Nou.

"Koda ban zama dan kwallo ba, to da na zama wani jami'i a fagen kwallon kafa" a cewar Pique a hirarsa da jaridar El Mundo Deportivo.

"Idan kana sha'awar kwallon kafa, to koda yaushe ita ce za ta kasance a ranka. Ba zan daina harkar kwallo ba koda na yi ritaya, fata na shi ne na zamo shugaban Barcelona."

Dan wasan mai shekaru 24 ya fito ne daga kungiyar rainon matasan 'yan kwallo ta Barcelona, sannan ya koma kungiyar bayan ya shafe shekaru hudu a Manchester United.