Fulham ta buga kunnen doki da Man City

Image caption 'Yan wasan Fulham suna murnar zura kwallo

Fulham ta buga kunnen doki da Manchester City, inda kungiyoyin biyu suka tashi biyu da biyu a filin wasa na Craven Cottage a gasar Premier ta Ingila.

Manchester City ce ta fara zura kwallaye biyu a ragar Fulham, kafin itama ta farke.

Sergio Aguero ya zura kwallaye biyu a wasan abun da kuma ya kawo adadin kwallayensa zuwa takwas a gasar Premier ta Ingila.

City ce ta fi mamaye wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma Bobby Zomara na fanshe kwallo guda ana minti 55, sai Fulham ta farfado.

Danny Murphy ne kuma ya zura kwallo ta biyu bayan Vincent Kompany ya taba ta.