Mourinho ya bada kyautar lambar yabonsa na zakaran koci

Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya bada kyautar lambar yabon da hukumar kwallon Turai ta ba shi a matsayin zakaran kocai-kocai a lokacin da ya lashe gasa uku a kungiyar Inter Milan.

Mourinho dai ya bada lambar yabon ne ga gidauniyar tunawa da Marigayi Bobby Robson.

Tsohon kocin Ingila da Barcelona Bobby Robson, ya mutu ne sanadiyar ciwon sankaran hunhu shekaru biyu da su ka wuce yana shekara 76 da haihuwa.

Kocin ne dai ya taimakwa Mourinho shiga harkar kwallon kafa.

Za'a kuma siyarda lambar yabon ne, inda za'a yi amfani da kudin wajen taimakawa masu ciwon sankaran mama da gidauniyar ke kula da su.

"Muna matukar murna da wannan karamci da Mourinho ya yi mana." In ji Mark dan marigayi Robson.