Arsenal ba za ta sallami Wenger ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Arsene Wenger

Shugaban Arsenal Ivan Gazidis ya ce kungiyar ba za ta sallami Arsene Wenger ba, duk da matsalolin da take fuskanta.

Arsenal dai bata yi nasara a wasanni uku cikin biyar da ta buga ba a gasar ta Premier ta bana, a yayinda take matsayi na 17 akan tebur.

Amma Gazidis ya ce: "Arsene Wenger na nan da martabarsa, bai kamata ana sukar sa ba, wannan wani komawa bayane ga harkar kwallon kafa."

"Ba ma tunanin sallamansa, saboda muna nan daram a gasar Premier babu yadda za'a yi a rage mana matsayi."

Gazidis ya kara da cewa: "Ba wai rana tsaka kawai za'a ce bai da kwarewa ba, wannan maganar banza ce."

Arsenal ta sha kashi ne da ci hudu da uku a hannu Blackburn a karshen mako, wanda hakan ke nufi, wannan ne karo farko da kungiyar ba ta fara da kafar dama ba, tun shekarar 1953.

Gazidis dai yace yana da kwarin gwiwar kan Wenger, inda ya ce kocin zai dawo da martabar kungiyar.