Villas-Boas ya kai karar alkalan wasa

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya kai kara wurin shugaban alkalan wasa na Ingila, Mike Riley game da yadda alkalan wasan suka tafiyar da wasan da kungiyar ta sha kashi a hannun Manchester United a ranar Lahadi.

Kwallaye biyun da Marchester United ta fara zurawa na nuni da cewa 'yan wasanta sunyi kwanten gida ne.

Villas-Boas ya ce: "A gaskiya ban ji dadi ba kan yadda alkalan wasan suka tafiyar da wasan, abu da kuma ya shafi makomar mu.

"Gaskiya baza mu bari ya wuce haka ba, kamata ya yi ace kowa ya yi aikinsa."

Tsohon kocin Porto mai shekarun haihuwa 33 ya kara da cewa:"Na kara gaba kuma na tattauna da mutanen da suka kamata."

"Gwiwar mu tayi sanyi akan alkalan wasan, abun da kuma yasa aka doke mu kenan."

Kashin da Chelsea ta sha a filin Old Trafford ita ce rashin nasara ta farko da aka yiwa Villas-Boas tun da ya kama aiki a Chelsea.