Didier Drogba na yakin neman zaman lafiya a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Didier Drogba

Dan wasan kasar Ivory Coast da kuma Chelsea, Didier Drogba ya shaidawa BBC yana kokarin ganin a wanzar da zaman lafiya a kasarsa bayan rikicin siyasa da aka yi a kasar.

Dan wasan na magana ne game da rawar da zai taka a kwamitin sulhu da zaman lafiya da gwamnatin kasar ta kafa, wanda kuma shi memba ne a ciki.

Ya ce baiyi wata-wata ba a lokacin da aka bayyana cewa yana kwamitin amma ya kara da cewa;" Akwai kalubale a gaba na amma zan ga inda karfi na ya kare."

Kusan mutane 3,000 ne suka mutu a yayinda 500,000 suka jikkata a rikicin siyasar da akayi a kasar na tsawon watanni hudu bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamban bara.

Drogba, na wakiltar 'yan kasar Ivory Coast ne dake zaune a kasashen waje a kwamitin mutane 11 da gwamnatin kasar ta kafa, domin tabbatar da sulhu a kasar.

"Ina fata cikin nan da wasu 'yan shekaru, mutane daga kudanci da kuma arewacin kasar daga kabilu dabam dabam za su hada kai, su kuma sassanta tsakaninsu." In ji Drogba.