Bob Bradley ne sabon kocin Masar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bob Bradley

Tsohon kocin Amurka, Bob Bradley ya sa hannu a kwantaragi a matsayin saboon kocin Masar.

Kocin zai jagoranci babbar tawagar, kasar ne har zuwa shekarar 2014, indan an kammala gasar cin kofin duniya a Brazil.

Bradley ya cimma yarjejeniya ne da Hukumar kwallon Masar a birnin alkahira.

A ranar asabar ne kocin zai gana da manema labarai, domin ya bayyana shirye-shiryensa ga tawagar kasar.