Hargreaves na murnar dawowa taka leda

Image caption Owen Hargreaves a lokacin da yake Manchester United

Dan wasan Manchester City Owen Hargreaves ya nuna farin cikinsa na dawowa taka leda bayan ya dan jimma yana jinya.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 30, ya taka leda na kusan sa'a daya kafin a sauya shi, a wasan da kungiyar ta doke Birmingham a gasar cin kofin Carling.

Owen Hargreaves ne ya fara zura kwallo farko a wasan.

Hargreaves ya ce: "Ban taba za ta zan iya dawowa harkar kwallon kafa, kamar yadda na dawo ba, gaskiya na yi matukar farin ciki."

Manchester United ta sallami dan wasan ne saboda yadda yake ta fama da rauni.

Dan wasan ma ya nemi ya buga mata a kyauta amma kungiyar taki amincewa da hakan.

A yanzu haka dai sai ya buga wasa ne a City za'a biya sa.