Ribery ya ce yana son ya gama taka leda a Bayern

Image caption Frank Ribery

Dan wasan Faransa da Bayern Munich Franck Ribery ya ce akwai yiwuwar ya gama taka leda a kungiyar Bayern Munich a Jamus.

Dan wasan dai ya ce yana jin dadin yadda yake taka leda a karkashin kocin kungiyar, Jupp Heynckes. Ribery mai shekarun haihuwa 28 ya dawo Bayern ne daga Marseille a shekarar 2007.

Dan wasan dai ya yi dan fama da rauni a karkashin tsohon kocin kungiyar Loius van Gaal, abun da kuma ya kawo masa koma baya.

A yanzu haka dai ya dawo kan ganiyarsa, inda ya zura kwallaye uku a wasanni shida da ya buga a gasar Bundesliga.

"Ina matukar murna da taka leda a Munich, kuma iyalina na jin dadin garin." In ji Ribery.

"Akwai yiwuwar ana kungiyar zan gama taka leda."