Fabregas ya na taimaka min - Xavi

Fabregas ya na taimaka min - Xavi
Image caption Fabregas ya koma Barcelona ne daga Arsenal

Dan wasan Barcelona Xavi ya yabawa Cesc Fabregas inda ya ce tsohon dan wasan na Arsenal ya na taimaka masa wajen taka leda yadda ya kamata.

Da farko an nuna shakku kan ko 'yan wasan biyu za su iya taka leda a lokaci guda lokacin da Fabregas ya koma Barcelona daga Arsenal.

"Ina ganin Cesc ya taimaka min wajen taka leda yadda ya kamata, kuma ina ganin mun karbi juna yadda ya dace," kamar yadda Xavi ya shaida wa shafin intanet na kulob din.

"Idan ya tafi gaba sai na tsaya a baya, ko kuma shi ma ya yi min hakan. Ina jin dadi idan ina filin kwallo kuma shi ma haka. Mun nuna haka a lokuta da dama a bana."

Daga nan kuma dan wasan ya bayyana cewa yarjejeniyar tallan da Barcelona za ta kulla da Qatar Foundation za ta taimaki kulob din matuka.

"Ina ganin za ta taimakawa Qatar ta fito da kimarta a duniya kuma muma za ta taimaka mana sosai."

Yarjejeniyar na daya daga cikin abubuwan da za a tattauna a babban taron kulob din da za a yi ranar Asabar.