EPL:City,Chelsea da Arsenal sun samu nasara

epl
Image caption Gasar premier ta Ingila

A karon farko tunda aka fara gasar premier ta Ingila a kakar wasa ta bana, Manchester United bata samu nasara ba a karawatta da abokiyar hammaya, inda ta tashi kunen doki wato daya da daya tsakaninta da Stoke City.

Kenan a halin yanzu Manchester City ta kamo United a yawan maki amma yawan kwallaye ne ya raba kulob din biyu. Har yanzu Chelsea ce ta uku akan tebur bayan ta lallasa Swansea daci hudu da daya.

Sakamakon karawar gasar premier na karshe mako:

*Manchester City 2 - 0 Everton *Arsenal 3 - 0 Bolton Wanderers *Chelsea 4 - 1 Swansea City *Liverpool 2 - 1 Wolverhampton Wanderers *Newcastle United 3 - 1 Blackburn Rovers *West Bromwich Albiom 0 - 0 Fulham *Wigan Athletic 1 - 2 Tottenham Hotspur *Stoke City 1 - 1 Manchester United