La Liga:Messi da Ronaldo sun haskaka

ronald da messi
Image caption 'Manya maganin kanana' Messi da Ronaldo

Bayan makwanni biyar ana fafatawa a gasar La Liga ta Spain, har yanzu Real Betis ce ke jan ragama akan tebur.

Amma kuma ana cigaba da rige rigen zira kwallaye tsakanin Lionel Messi na Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid inda kowannensu ya zira kwallaye uku a wasan da suka buga ranar Asabar.

Messi yaci kwallaye uku a wasan da suka lallasa Atletico Madrid daci biyar da nema a yayinda Ronaldo shima yaci kwallo uku a wasan da suka doke Rayo Vallecano daci shida da biyu.

A halin yanzu Messi yaci kwallaye takwas a gasar La Liga ta bana sai kuma Ronaldo na biyu mai kwallaye bakwai.

Sauran wasanni:

*Sevilla 1 - 0 Valencia *Athletic Club 1 - 1 Villarreal *Mallorca 2 - 1 Real Sociedad *Barcelona 5 - 0 Atl├ętico Madrid *Real Madrid 6 - 2 Rayo Vallecano