Rooney zai yi jinyar fiye da mako daya

rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wayne Rooney

Wayne Rooney ba zai buga wasanni Manchester United biyu masu zuwa ba, kamar yadda kocinsa Sir Alex Ferguson ya bayyana, inda yace dan kwallon zai yi jinya fiye da mako guda.

Dan wasan Ingilan bai buga wasansu da Stoke ba saboda rauni a kafadarsa.

Kenan Rooney ba zai buga wasan United da Basel a gasar zakarun Turai a ranar Talata da kuma wasan premier tsakaninsu da Norwich City a karshen mako mai zuwa.

Ferguson yace "raunin ba mai tsanani bane amma kuma zai yi jinyar fiye da mako guda".

Wato babu tabbas ko Rooney zai bugawa Ingila wasanta da Montenegro a ranar bakwai ga watan Oktoba.

Kenan a yanzu 'yan wasan United dake jinya sun hada da Nemanja Vidic, Chris Smalling, Rafael da Silva, Tom Cleverley, Darron Gibson, John Evans da kuma Michael Carrick.