Matsin tattalin arziki zai shafi tamola

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Arsene Wenger ya koka kan rashin halartar 'yan kallo

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce rashin nasara ne ya taimaka wajen rashin halartar 'yan kallo da yawa a wasansu da Bolton na ranar Asabar.

Sai dai kocin na Arsenal ya yi gargadin cewa matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a duniya zai haifar da karancin 'yan kallo a kakar bana.

"Da farko mun fuskanci rashin nasara, abu na biyu kuma ana fuskantar matsalar tattalin arziki,"a cewar Wenger.

"Za a rinka samun karancin 'yan kallo, kuma tuni mun fara fahimtar hakan."

An ga kujerun da babu kowa da dama a wasan da Arsenal ta doke Bolton da ci 3-0 a filin wasa na Emirates.

Robin Persie ne dai ya zira kwallaye biyu yayin da Alex Song ya ci ta uku.