Rooney da Hernandez ba zasu bugawa United ba

Hernandez and Rooney Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hernandez da Rooney

Manchester United zata buga wasanta na gasar zakarun Turai banda Wayne Rooney tsakaninta da Basel a ranar Talata.

Dan wasan mai shekaru 25 zai yi jinyar akalla mako guda saboda rauni a kafadarsa.

Haka zalika Javier Hernandez da Chris Smalling, Jonny Evans, Nemanja Vidic, Rafael da kuma Tom Cleverley duk ba zasu buga ba saboda rauni.

Evans na fama da rauni a idon sawunsa a yayinda Vidic keda ciwo a kafarsa.

A wasanta na farko a gasar zakarun Turai, United ta tashi kunen doki ne tsakaninta da Benfica.