Ba zan gaggauta sabunta kwangila ba-Van Persie

van persie
Image caption Robin Van Persie

Dan kwallon Arsenal Robin van Persie ya ce baya gaggawar tsawaita kwangilarsa don shafe lokaci mai tsawo tare da kulob din.

Dan wasan mai shekaru 28 wanda shine kyaftin din kulob din a kakar wasa ta bana, yanada sauran shekaru biyu kafin kwangilarsa ta kare a Emirates.

Kocin kulob din Arsene Wenger yanason yasamu tabbaci akan van Persie tun bayan tafiyar Cesc Fabregas da Samir Nasri.

Van Persie yace"ba na tunanin abinda ya dace ne inyi maganar sabuwar kwangila a kakar wasa ta bana".

Idan har Van Persie yaki sabunta yarjejeniyarsa da Arsenal, tabbas hakan cikas ne ga kulob din saboda ganin cewar manyan 'yan wasanta sun fice kafin kakar wasan data wuce.