Laudrup ya raba gari da Mallorca

laudrup
Image caption Micheal Laudrup

Michael Laudrup ya ajiye mukaminsa a matsayin kocin kungiyar Mallorca ba tare da bata lokaci ba sakamakon korar mataimakinsa Erik Larsen.

A ranar Litinin ne aka kori Larsen a Mallorca bayan ya fito fili a soki mai kulob din Lorenzo Serra Ferrer a wata tattaunawa a jaridar kasar Denmark.

Laudrup wanda tsohon dan wasan Barcelona da Real Madrid ne yana takun saka tsakaninsa da mai kulob din tun lokacin batun kasuwar musayar 'yan kwallo.

A yanzu dai Laudrup ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda.

Tun a watan Yulin 2010 ne aka nada Laudrup a matsayin kocin Mallorca kuma a bisa tsari kwangilarsa zata kare ne a karshen kakar wasa ta bana.