'Yan sanda sun damke Bramble na Sunderland

bramble
Image caption Titus Bramble

An damke dan wasan Sunderland Titus Bramble bisa zargin cin zarafi da kuma mallakar haramtacciyar kwaya.

A halin yanzu 'yan sanda a garin Teeside sun tsare dan kwallon mai shekaru talatin.

Rundunar 'yan sanda a Cleveland ta ce an kama Bramble ne da sanyi safiyar ranar Laraba.

Sanarwar da Sunderland AFC ta fitar ta ce "kulob din na duba lamarin akan binciken da 'yan sanda ke yi".

Bramble ya soma kwallo ne tare da kulob din Ipswich kuma ya bugawa Ingila kwallo sau goma a matakin 'yan kasada shekaru 21.

Ya taka leda a Newcastle da Wigan kafin ya koma Sunderland a shekara 2010.