Anzhi ta nada Carlos a matsayin kocin riko

carlos
Image caption Roberto Carlos

Kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha ta nada Roberto Carlos a matsayin kocin riko bayan korar Gadzhi Gadzhiyev a matsayin koci.

Anzhi ta samu nasara ne a wasa daya tala cikin wasanni shida da suka wuce duk da zuwan Samuel Eto'o daga Inter Milan kuma ita ce ta bakwai akan teburin gasar kasar.

Rahotanni daga Brazil sun nuna cewar Roberto Carlos zai hada mukamin kocin riko ne sannan kuma ya shiga fili ya taka leda da sauran 'yan kwallo.

Roberto Carlos mai shekaru 38 ya koma Anzhi ne a matsayin dan kwallo a watan Fabarairu a kwangilar shekaru biyu da rabi.

A halin yanzu Andrey Gordeyev zai kasance mataimakinsa.