Adamu zai gurfana gaban CAS a ranar Talata

amso
Image caption Amos Adamu

A ranar Talata ne Amos Adamu zai bayyana a gaban kotun sauraron kararrakin wasanni a mataki na karshe don sauya dakatarwar shekaru uku da aka yi masa daga shiga harkar kwallon kafa.

Kotun sauraron kararaki wasanni wato CAS zata ji ba'asin dan Najeriya din akan dakatarwar da aka yi mashi daga kwallo.

Kwamitin da'a na Fifa ya dakatar da Adamu bayan an kamashi da laifin kokarin karbar cin hanci a zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 da kuma 2022.

An dakatar da Amos Adamu ne tare da dan Mali Amadou Diakite da kuma dan kasar Tonga Ahongalu Fusimalohi a watan Nuwamban bara.