Capello bai gayyaci Ferdinand a Ingila ba

capello
Image caption Fabio Capello

Ba a gayyaci dan kwallon Manchester United Rio Ferdinand ba cikin tawagar 'yan wasan Ingila da zata fafata da Montenegro a wasan share fage na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai a 2012.

Amma dai an gayyaci dan wasan Liverpool Andy Carroll, dana Fulham Bobby Zamora da kuma na Manchester United Danny Welbeck amma kuma banda Jermain Defoe na Tottenham.

Haka zalika banda kyaftin din Liverpool Steven Gerrard.

Tawagar da Fabio Capello ya gayyata:

Scott Carson (Bursaspor), Joe Hart (Man City), David Stockdale (Ipswich); Leighton Baines (Everton), Gary Cahill (Bolton), Ashley Cole (Chelsea), Phil Jagielka (Everton), Phil Jones (Man Utd), Micah Richards (Man City), John Terry (captain, Chelsea), Kyle Walker (Tottenham); Gareth Barry (Man City), Stewart Downing (Liverpool), Adam Johnson (Man City), Frank Lampard (Chelsea), James Milner (Man City), Scott Parker (Tottenham), Theo Walcott (Arsenal), Ashley Young (Man Utd); Darren Bent (Aston Villa), Andy Carroll (Liverpool), Wayne Rooney (Man Utd), Danny Welbeck (Man Utd), Bobby Zamora (Fulham)