Dan kwallon Arsenal Sagna ya karya kafarsa

sagna
Image caption Bacary Sagna

Dan kwallon Arsenal Bacary Sagna zai yi jinyar akalla watanni uku bayan ya karya kafarsa a wasansu da Tottenham a ranar Lahadi.

Sai da aka cire Sagna a cikin fili bayan ya yi taho mu gama da Benoit Assou-Ekotto, a wasan da Spurs ta casa Gunners daci biyu da daya.

A ranar Litinin za a yiwa Sagna gyaran karayar daya samu a kafar tasa.

Wannan jinyar ta nuna cewar Sagna ba zai buga wasanni Faransa na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai ba da za ayi tsakaninta da Albania da kuma Bosnia-Herzegovina.

Sagna yabi sawun sauran 'yan kwallon Arsenal dake jinya mai tsawo kamarsu Jack Wilshere, Thomas Vermaelen, Abou Diaby da kuma Johan Djourou.

Bisa dukkan alamu Carl Jenkinson da aka siyo daga Charlton shine zai maye gurbin Sagna a Arsenal.