Kotu ta baiwa wata Mata nasara akan gasar premier

kareb
Image caption Karen Murphy

Wata mata da ke da gidan giya a nan Ingila ta sami wata nasara a kotu a kan Hukumar Kwallon Kafa ta Premier League a nan Ingila game da duniya wasannin kwallon kafan a talabijin.

Wannan hukunci dai yana da tasiri mai yawa a kan makomar watsa wasan kwallon kafar ta kafofin labarai a Biritaniya da Turai.

Kotun Turai ta yanke hukuncin cewa dokar kasar, wadda ta hana Karen Murphy yin amfani da tashar talabijin ta kasar Girka a gidan giyarta don nuna wasan, ta saba ma 'yancin da take da shi na biyan bukatar masu sayayya daga gare ta, babu kuma wata hujja ta aiki da ita.

Wakilin BBC ya ce hukuncin zai zafafa gasa tsakanin kafofin watsa labarai, tare kuma da tilasta wa Hukumar Kwallon Kafar ta sauya yadda take sayar wa kafofin labarai iznin nuna wasan.